1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SPD za ta fidda dan takara a watan Janairu

November 21, 2016

Jam'iyyar SPD a Jamus ta ce za ta yi aiki cikin natsuwa kafin tsayar da dan takarar neman mukamin shugaban gwamnati wanda za a yi zabe kansa a cikin shekara mai kamawa.

https://p.dw.com/p/2T2CV
Deutschland SPD-Parteikonvent in Wolfsburg
Martin Schulz da Sigmar Gabriel a gun wani babban taron SPD a garin WolfsburgHoto: picture-alliance/dpa/J. Stratenschulte

Jam'iyyar SPD da ke cikin gwamnatin kawancen Jamus ta ce a farkon shekarar 2017 za ta yanke shawara game da wanda za ta tsayar takarar nemen mukamin shugaban gwamnatin Jamus. Majiyoyin jam'iyyar a birnin Berlin sun nuna cewa a gun babban taron manyan shugabanninta a karshen watan Janerun 2017 za a tsayar da dan takarar. Shugabanta Sigmar Gabriel da shugaban majalisar dokokin Turai Martin Schulz ke kan gaba a jerin 'yan takarar. Da farko Firimiyar jihar North-Rhein Westfalia, Hannelore Kraft 'yar jam'iyyar SPD, ta ce za su yi aiki cikin tsanaki.

Ta ce: "Social Democrat jam'iyya ce mai ji da kanta. Tsarin lokacinta bai dogara kan lokacin da CDU da CSU suka tsayar da dan takara ba. A saboda haka za mu tattauna da juna cikin tsanaki, kun san dokokinmu ba bu kuma abinda ya canja a ciki."

A wannan Lahadi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, 'yar jam'iyyar CDU, wadda tun a shekarar 2005 ke rike da wannan mukami ta ce za ta sake yin takara karo na hudu a jere.