1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Steinmeier a MDD

YAHAYA AHMEDNovember 29, 2005

Sabon ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya kai ziyararsa ta farko a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya, inda kuma ya gana da babban sakataren majalisar Kofi Annan.

https://p.dw.com/p/Bu3r
Steinmeier
SteinmeierHoto: AP

A lokacin da ya gana da Kofi Annan, ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya mika gaisuwar sabuwar gwamnatin Jamus ga babban sakataren na Majalisar Dinkin Duniya, inda kuma ya tabbatar masa da cewa, Jamus za ta zarce ne da manufofin siyasarta na ketare. Ya kara da cewa:-

„Za mu ci gaba da ba da gudummuwarmu, saboda bisa al’adar manufofin siyasar harkokin wajen Jamus, muna mai da alkiblarmu ne ga akidar ribanya huldodi; kuma ta hakan ne muke aiwatad da manufofinmu. Ba a huskar kare zaman lafiya kamar a Afghanistan kawai muke bayyana ba. A bangarori da dama, kamar dai wajen karbar bakwancin muhimman taruka irin wanda aka yi a fadar Petersberg, na share fagen kafa gwamnati a Afghanistan ko kuma taron kasa da kasa na kafa na’urorin lura da aukuwar annobobi, wanda za a yi a shekara mai zuwa, muna ba da gudummuwarmu.“

Wannan ci gaba da manufofin siyasar ketare dai na kuma bukatar ganin cewa Jamus ta sami kujerar dindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, inji ministan:-

„Har ila yau dai batun yi wa kwamitin sulhun garambawul na kan ajandar tarukan da Majalisar Dinkin Duniyar za ta yi, abin da ya kunshi fadada wannan kwamitin. Muna nan dai muna bin burinmu, kuma bisa kiyasin da muka yi, da akwai alamun cewa za mu sami goyon baya mai rinjayi.“

Steinmeier dai ya ce sai a farkon watan Disamba ne za a ga yadda ababa za su kasance a taron majalisar da za a yi. A nan ne kuma, za a tsai da shawarar yin muhawara kan bukatu daban-daban da aka gabatar, alal misali kan matsayin da kasashen nahiyar Afirka suka dauka game da batun fadada kwamitin sulhun. A tattaunawar da suka yi, Steinmeier da Kofi Annan, sun amince da muhimmancin rawar da alkalin nan na Jamus Mehlis ke takawa, wajen gudanad da bincike kan kisan gillar da aka yi wa tsohon Firamiyan kasar Lebanon Rafik Hariri. Ministan harkokin wajen na Jamus ya kuma tabbatar wa Kofi Annan cewa kasarsa, tare da hadin gwiwar Faransa da Birtaniya da kuma Amirka na nan na ta kokarin samo hanyoyin magance rikicin da ake yi kan batun makamashin nukiliyan Iran, a huskar diplomasiyya.

Ministan ya kuma bukaci Amirka da ta ba da haske kan zargin da ake yi wa kungiyar leken asirinta, wato CIA, na tsare fursunonin yaki da kuma gallaza musu a wasu sansanonin sirri a nahiyar Turai. Bayan ganawarsa da wakilan kungiyoyin Yahudawa a birnin na New York, Stzeinmeier ya tashi zuwa birnin Washington, inda a yau ne zai gana da da takwarar aikinsa ta Amirka, Condoleeza Rice a karo na farko.