1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Steinmeier a Rasha.

December 5, 2005

A ran asabar da ta wuce ne ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya kai ziyararsa ta farko a birnin Moscow, inda ya yi shawarwari da shugabannin Rasha.

https://p.dw.com/p/Bu3g
Steinmeier
SteinmeierHoto: AP

Tun da aka kafa sabuwar gwamnati a birnin Berlin ne, masu kula da huldodin dangantaka tsakanin Jamus da Rasha suka sami kansu cikin wani hali na rudami, saboda rashin sanin irin kamun ludayin da sabuwar shugaban gwamnatin Angela Merkel za ta yi game da manufofin harkokin siyasarta na ketare, musamman ma dai dangane da huldodi tsakaninta da mahukuntan Rasha. Amma ziyarar da sabon ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmeier, ya kai a birnin Moscow a ran asabar da ta wuce, ta share fagen zarcewa da huldodi tsakanin kasashen biyu kamar dai yadda suke a da.

Shi dai Steinmeier, ba farin shiga ba ne a fagen diplomasiyya, kuma sananne ne a birnin Moscow. A tsohuwar gwamnatin Gerhard Schröder dai, shi ne jagoran ofishin shugaban. Sabili da haka, ya san ko me ake ciki a huldodin diplomasiyya tsakanin kasarsa da Rasha. Wasu masharhanta ma na ganin cewa, shi ya jagoranci tsara manufofin siyasar ketare na Jamus game da ita Rashan. Ta hakan ne dai ake kyautata zaton cewa, a lokacin wa’adin wannan sabuwar gwamnatin ma, ba za a sami wani muhimmin sauyi a huldodin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ba. Duk da cewa dai sabuwar shugaban gwamnati Merkel ce, za ta zayyana alkiblar siyasar da Jamus za ta bi, za a dau wani tsawon lokaci kafin hakan ya samu.

Kyakyawar huldar dangantaka da ke tsakanin tsohon shugaban gwamnatin tarayya Gerhard Schröder da shugaba Vladimir Putin na Rsaha, yanzu ta koma bayan shinge. Babu shakka, yanayin wannan dangantakar zai sake bayan hawar Angela Merkel karagar mulkin Jamus.

Jami’an fadar Kremlin dai sun yi marhabin da ziyarar da Steinmeier ya kai a birnin na Moscow, inda kuma suka kyautata zaton cewa, za a zarce da huldodin dangatakar da ke tsakanin kasashen biyu. To sai dai, har ila yau, akwai masu nuna shakku ga samun kome ya tafi daaidai kamar a lokacin Gerhard Schröder. Manazarta al’amuran da ke kai suna kawowa a huldodi tsakanin kasashen biyu na ganin cewa, Merkel ba za ta rufe ido kan wasu illolin da ake zargin gwamnatin birnin Moscow da su ba; alal misali kamar danne hakkin maneman labarai, da take hakkin dan Adam a yakin da dakarun Rashan ke gwabzawa da `yan tawayen Checheniya.

A huskar kasuwanci dai, babu wani muhimmin sauyin da za a samu. Saboda har ila yau, Rashan dai ita ke bai wa Jamus mafi yawan hayakin gas da man fetur da take bukata. Game da hakan ne kuwa, kawo yanzu, Jamus ba ta fitowa fili ta yi kakkausar suka ga wasu ababan assha da ake zargin mahukuntan fadar Kremlin da aikatawa. Abin tambaya a nan dai shi ne, wai shin Angela Merkel za ta iya cika alkawarin da ta yi kuwa a lokacin yakin neman zabe, na cewa ba za ta ci gaba da hulda tsakanin Berlin da Moscow, wadda ke yi wa sauran kasashen yankin Baltik saniyar ware ba ? Za ta fadada huldodin Jamus ne da biranen Warsaw, da Riga da Talin da Vilnius, maimakon inganta ma’ammala da birnin Moscow ?

A ziyarar da ta kai a birnin Warsaw a makon da ya gabata, Angela Merkel ta nuna alamun daukan matakai a wannan huskar, da burin kwantar wa kasashen yankin Batik din hankali. Ta kuma ba da sanarwar kafa wani kwamiti, wanda zai yi nazarin yiwuwar bai wa kamfanonin wadannan kasashen wasu daga cikin kwangilar shimfida bututun hayakin gas a karkashin tekun Gabas, daga Rasha zuwa Jamus. Idan ko hakan ya yiwu, to zai kasance wani gagarumin nasara ke nan ga manufofin siyasar ketare ta Jamus.

To yanzu dai da aka gama hada-hadar zabe a nan Jamus, an komo ne ga harkokin siyasa na yau da kullum. Babu kuwa mai sha’awar ganin cewa, an sake samun sabani a huldodin dangantaka tsakanin Jamus da Rasha. A cikin watan Janairu mai zuwa ne dai shugaban gwamnatin tarayyar Jamus din, Angela Merkel da kanta, z ata kai ziyara a birnin Moscow, kuma a cikin watan Maris ne za a yi taron koli na gwamnatocin kasashen biyu a garin Tomsk.