1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta baiyana fatar samun nasara a tattaunawa da yan tawayen gabashin kasar

June 11, 2006
https://p.dw.com/p/BuuV

Gwamnatin kasar Sudan ta baiyana fatarta ta samun nasara a tattaunawar wannan mako tare da yan tawayen gabashin kasar.

Jakadan gwamnati Mustafa Osman Ismail bayan ganawarsu da shugaba Hosni Mubararrk na kasar Masar,ya baiyana cewa,gwamnatin Sudan tana fata tattaunawar ta ranar talata zata kawo karshen rikice rikice a kudanci da gabashin kasar,tare da baiwa Sudan damar mayarda hankalin akan sake gina kasar.

A watan daya gabata ne dai mataimakin shugaban kasar Sudan Ali Osman Taha da shugaban kungiyar tawayen gabashin kasar Musa Muhammad Ahmed suka sanya hannu kann wata yarjejeniya dta sake farfado da kokarin wanzar da zaman lafiya tsakaninsu.

A shekarar data gabata ne dai manyan kabilu na gabashin Sudan suka kirkiro da kungiyoyin tawaye na Beja da larabawan Rashidiya,wadanda suke da bukatu daya dana yankin Darfur,wato samun karin iko da kuma mallakar albarkatun da suke dasu a yankunansu.