1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta ce ba´a aikata kisan kare dangi a lardin Darfur

November 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvLJ

Mataimakin shugaban Sudan Ali Osman Taha ya ce rikicin lardin Darfur dake yammacin kasar na kabilanci ne kuma ba za´a iya kwatanta shi da wani kisan kare dangi ba. Bayan wani taro da suka yi da shugaban Masar Hosni Mubarak a birnin Alkahira, Taha ya fadawa manema labarai cewa rikicin Darfur na kabilanci ne da ruwansa da wani batun siyasa ko kisan kare dangi. Taha ya yi zargin cewa kasashen duniya na kara wa miya gishiri a dangane da rikici, yayin da irin wadannan rikice-rikice na kabilanci suka zama ruwan dare a nahiyar Afirka. Amirka ta bayyana abin da ke faruwa a Darfur da cewa kisan kare dangi ne da sojojin gwamnati da Larabawa ke yiwa bakar fata, sannan a farkon wannan shekara MDD ta fid da wani rahoto wanda ya ce ana cin zarafin ´yan Adam a Darfur to amma ba ta ce ana aikata kisan kare dangi ba.