1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta gayyaci UN zuwa yankin Darfur

May 11, 2007
https://p.dw.com/p/BuLe

Hukumomin Sudan sun gayyaci Majalisar Ɗinkin Dunia, ta aika tawaga ta mussamman a yankin Drafur, domin gani da iddo, halin da yan gudun hijra daga ƙasar Tchad ke ciki.

Shugaban hukumar yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Dunia da ya bada labarin, ya ce a tsukin wattani 3 da su ka gabata, yan gudun hijira kimanin dubu 45, su ka kwararo daga ƙasar Tchad, zuwa maƙwabciyar ta Sudan.

A ɗaya hannun kuma tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia da ƙungiar tarayya Afrika, na ci gabada ganawa da hukumomin Khartum, a game da hanyoyin aika rundunar shiga tsakani ta haɗin gwiwa zuwa yankinna Darfur.

Shugabanin tawagar, wato Salim Ahmed Salim da Antonio Guteres, sun kiri taron manema labarai, a birin Khartum inda su ka bayyana gamsuwa, a game da ci gaban da a ka samu, a tantanawa da gwamnatin Sudan don cimma burin da aka sa gaba.

A wani ci gaban kuma da a ka samu, ƙasar Sin da ke bada goyan baya ga Sudan, ta amince ta taimaka da sojoji a cikin wannan runduna.