1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu: Dakarun MDD sun gaza

Ahmed SalisuAugust 6, 2016

Wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fidda ya ce jami'an majalisar da ke aiki wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu sun gaza wajen kare fararen hula a sansanin Malakal.

https://p.dw.com/p/1JchT
Konflikt im Südsudan Ankunft bengalische UN-Soldaten 31.12.2013
Hoto: Reuters

Rahoton wanda aka fidda shi a jiya Juma'a ya ce masu aikin wanzar da zaman lafiya sun gaza aiwatar da aikin da ya kamata su yi na kare rayukan mutane lokacin da rikici da ke da kabilanci ya barke a yankin cikin watan Fabrairun da ya gabata inda mutane 30 suka rasu yayin da wasu 120 suka raunuka.

Har wa yau, kunshin rahoton ya ce ya na da tabbacin an kitsa wannan hari da aka kai mutanen da ke sansanin ne da sa hannun mayakan SPLA wadda ke samun tallafi daga gwamnatin Sudan ta Kudu. Wannan dai ya sanya kwamitin da ya gudanr da bincike yin kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta sake duba tsarin da ta ke da shi na kare fararen hula musamman ma wanda ke cikin hadari a irin wadannan wurare da ke fama da tashin hankali.