1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu ta shiga mawuyacin hali

Ahmed Salisu
April 8, 2017

Shugaba Salva Kiir Sudan ta Kudu ya ce kasar tana cikin yanayi na ja'ibar yunwa sakamakaon fari da kasar ke ciki.

https://p.dw.com/p/2aw0T
Äthiopien Addis Abeba Salva Kiir Mayardit und  Hailemariam Desalegn
Hoto: Getty Images/AFP/Z. Abubeker

A karon farko hukumomi a birnin Juba na Sudan ta Kudu sun bayyana cewar kasar na cikin ja'ibar yunwa kuma mutane da yawa ne a kasar musamman ma kananan yara wannan matsala ta shafa.

Shugaban Sudan ta Kudu din Salva Kiir ya ce gwamnatinsa za ta ware dala dubu hamsin domin tinkarar wannan warsaka kana za a yi amfani da kudaden da aka samu daga gudun nan na yada kanin wani da za a gudanar a kasar wajen kawar da matsalar ta yunwa.

A wani jawabi da ya yi ga al'ummar kasar, Shugaba Kiir ya ce ko shakka babu wannan matsala ta yunwa wadda karancin abinci ya haifar abu ne da za a iya gani karara a kasar.

Masu aiko da rahotanni suka ce alkaluman da ake da su a kasa na nuna kashi biyu bisa uku na al'ummar kasar da na cikin hali na bukatar abinci inda wasunsu ke cikin mawuyacin hali.