1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta musanta taimakawa yan tawayen Chadi

April 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1q

Shugaban ƙasar Sudan Omar al-Bashir ya musanta zargin cewa gwamnatin sa na marabawa yan tawaye baya, su hambarar da gwamnatin ƙasar Chadi. Al-Bashir ya kuma zargi gwamnatin Chadi da haddasa rashin kwanciyar hankali a kan iyakar ƙasashen biyu dake makwabtaka da juna. A karon farko da al-Bashir ya yi jawabi, tun bayan ɓarkewar tarzomar da ta auku a baya bayan nan a ƙasar Chadi, yace Sudan ba ta da wani nufi na tada zaune tsaye a ƙasar Chadi. A ranar jumaár da ta gabata Gwammnatin Chadi ta yanke hulɗar jakadanci da ƙasar Sudan bayan da yan tawaye suka kai farmaki birnin Ndjamena babban birnin ƙasar Chadi wanda ya yi sanadiyar mutuwar a ƙalla mutane 400. Gwamnatin Chadi ta kuma sanar da cewa za ta rufe kan iyakar ta da ƙasar Sudan.