1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta yi watsi da zargin da ake yi mata na saɓa wa yarjejeniyar Darfur.

May 22, 2006
https://p.dw.com/p/BuxH

Ƙasar Sudan ta yi watsi da zargin da ’yan tawayen Darfur ke yi mata, na kai hari kan sansaninsu, abin da ya saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta da ta zaman lafiyar da aka cim ma a birnin Abujan Najeriya, da nufin kawo ƙarshen rikicin yankin, wanda tuni ya janyo asarar rayukan dubban jama’a.

An dai sanya hannu kan yarjejeniyar ne, tsakanin gwamnatin Sudan ɗin da babbar ƙungiyar ’yan tawayen yankin, bayan anagazawar da gamayar ƙasa da ƙas ata yi musu. A jiya ne dai, ƙungiyar da Minni Arcua Minnawi ke yi wa jagoranci, wadda ta sanya hannu kan yarjejeniyar, ta zargi gwamnatin Sudan da ’yan kurarta, wato ƙungiyar nan ta Janjaweed da kai mata hari a sansaninta da ke Dar es Salaam a arewancin yankin na Darfur.

Amma kakakin rundunar sojin Sudan ɗin, a cikin wata sanarwar da ya bayar yau a birnin Khartoum, ya yi watsi da wannan zargin, da nanata cewa, babu wani rukunin soji da ya kai hari a yankin. Raɗe-raɗi kawai ake ta yayatawa. Amma babu wani ƙashin gaskiya a cikin zargin da ake yi musu.

Ƙungiyar Tarayyar Afirka, wato AU, ta ce, an lura da rukunan ’yan ƙungiyar Janjaweed suna ta taruwa a arewaci da kuma kudancin yankin na Darfur, inda aka sami musayar wuta tsakaninsu da dakarun ’yan tawayen. Sai dai ta ce ba za ta iya tabbatarwa ba ko sojojin gwamnatin Sudan ma, sun kai wa ’yan tawayen hari.