1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta zargi wasu daulolin duniya da yi mata zagon kasa

January 22, 2006
https://p.dw.com/p/BvB7

A yau lahadi jajiberen wani taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU, shugaba Omar al-Bashar ya dan sassauto dangane da kokarin da Sudan ke yi na shugabantar kungiyar. Shugaba Bashar ya yi zargin cewa wasu ke shirya makarkashiyar yiwa gwamnatinsa zagon kasa. Bashar yace muhimmin batu shine samun nasarar kungiyar ta AU amma ba darewa kan kujerar shugabanta ba. Shugaban ya zargi wasu dauloli da nunawa Sudan adawa dangane da takarar shugabantar AU. Bisa ga alama dai shugaban na hannunka mai sanda ne ga Amirka, wadda ta ce bai kamata Sudan ta jagoranci kungiyar AU ba a daidai lokacin da kungiyar ke kokarin yin sulhu a rikicin lardin Darfur. A gobe ne shugabannin kungiyar mai membobi 53 zasu yanke shawara kan ba wa Sudan shugabancin kungiyar a wajen taron kolin da za´a fara a birnin Khartoum. Amma majiyoyi sun ce ana iya ba Kongo ko kuma a shawo kan Nijeriya ta yi ta zarce a kan kujerar shugabancin kungiyar ta AU.