1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan tayi fatali da hukuncin kasa da kasa

February 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuQy

Kasar Sudan tace ba zata amince da halalcin shawarar kotun kasa da kasa mai sauraron laifukan yaki ba,wanda tun farko a yau ta sanarda sunayen mutane biyu da zargin aikata laifukan yaki a lardin Darfur.

Babban alkali na kotun Luis Moreno Ocampo ya umurci alkalan kotun da su aike da takardun sammacin tsohon ministan harkokin cikin gida na Sudan Ahmed muhammad Harun da shugaban Janjaweed Ali Kushayb da ake zargi da kisan kiyashi da fyade da sauran dangogin azaba ga jamaar Darfur.

Alkalin yace yana ci gaba da bincike kann taasa da aka aikata a Darfur.

A nata bangare Sudan tace itace zata gurfanar da wadanda suka aikata laifin da kanta ba wata kasa ba.