1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan: Zargin amfani da makamai masu guba

September 29, 2016

Kungiyar kare hakkin jama'a ta Amnesty International ta zargi sojin Sudan da hari da makamai masu guba a lardin Darfur.

https://p.dw.com/p/2QiTR
Adriane Ohanesian Fotografin
Hoto: picture-alliance/Adriane Ohanesian/Handout

Kungiyar kare hakkin jama'a ta kasa da kasa ta Amnesty International, ta ce akwai alamun cewar gwamnatin kasar Sudan ta kai hare-haren makamai masu guba 30 a garin Jebel Marra da ke lardin Darfur, tun daga watan Janairu, kamar yadda kwararru ke zargi.

Kungiyar fafutukar ta kiyasta cewar a kalla mutane 250 ne suka mutu, wadanda ake zargin mutuwar da nasaba da makamai masu guba da aka yi amfani dasu wajen kai hare haren. 

A wata sanarwar daya gabatar, jakadan Sudan a Majalisar Dunkin Duniya Omer Dahab Fadl Mohamed, ya ce zargin na Amnesty ba shi da wani tushe, domin Sudan bata mallaki ko wane irin makami mai guba ba.