1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Suka kan ƙasar Masar

November 26, 2010

An yi suka bisa ƙuntatawa abokan hamayya da gwamnatin Masar ke yi, gabanin zaɓen ƙasar .

https://p.dw.com/p/QJew
Wani Ba-Misire ke nuna misali da halin da 'yan adawan kasar ke cikiHoto: AP

Jam'iyun adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama sun soki manufar takurawa abokan hamayya a ƙasar. A ɓangaren ta ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta ƙasa da ƙasa wato Amnesty International, ta yi ƙira ga gwamnatin ƙasar Masar da ta saki mutumin da take tuhuma, kan yin amfani da dandalin sadarwa ta Facebook. Ƙungiyar Amnesty tace bisa ga labarin da ta ke da shi, wanda ake tuhumar Ahmed Hassan Bassyouni, ya rubuta wani labari ne wanda kuma ba ɓoyyaye bane, kana an sha buga labarin a jaridun ƙasar, amma yanzu ana yi masa bita da ƙulli sabo da wata manufa ta daban. Gwamnatin ƙasar dai ta gurfanar da Bassyoun a gaban kotun soji, inda take tuhmarsa da yaɗa bayanan sirri na sojojin ƙasar. Idan dai aka samu Bassyoun da laifi, yana iya fiskatar ɗaurin shekaru biyar a gidan yari. Ƙungiyar Amnesty ta buƙaci gwamnatin ƙasar Masar dake samun goyon bayan ƙasashen yamma, da ta kawo ƙarshen hukunta fararen hula a kotun sojoji. A yan makwanin nan dai an kame daruruwan 'yan adawa a ƙasar ta Masar, gabanin zaɓen 'yan majalisar dokoki.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Zainab Muhammed Abubakar