1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sukar furucin shugaban Iran na kawad da Isra´ila daga doron kasa

October 28, 2005
https://p.dw.com/p/BvNa

Duk da sukar da take sha daga kasashen duniya Iran ta ci-gaba da kamfen nuna adawa da wanzuwar kasar Isra´ila. Kamfanin dillancin labarun Iran ya rawaito ministan harkokin wajen kasar Manusher Mottaki na saka ayar tambaya dangane da halaccin wanzuwar kasar Bani Yahudu. Kamar yadda aka saba bisa al´adar juyin juya halin Islama a kasar ta Iran, mahukunta sun yi kira ga al´umar kasar da su shiga wata zanga-zangar yin Allah wadai da Isra´ila a yau juma´ar karshe ta azumin watan ramadan wannan shekara. A ranar laraba da ta wuce shugaban Iran Mahmud Ahmedi-Nejad ya fito fili yayi kira da a gusar da Isra´ila daga doron kasa. Wadannan kalamai na sa ya sha suka da kakkasuar harshe daga kasashen duniya. Babban sakataren MDD Kofi Annan ya ce ya kadu da jin wadannan kalaman. Sannan gwamnatin birnin Berlin da sauran gwamnatocin Turai sun nemi jakadun Iran a kasashen su da su yi musu bayani game da furucin na shugaba Ahmedi Nejad. Ita ma hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinawa ta yi tir da kalaman na shugaban Iran.