1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sulhu tsakanin Hamas da Fatah

April 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0y

Shugaban hukumar palestinawa Mahamud Abbas, tare da shika shikan Hamas, sun cimma daidaito, da sanhin sahiyar yau, a kan wajibcin fahintar junan su.

Ranar jiya ,idan ba a manta ba, magoyan bayan ɓangarorin 2 sun ba hammatoci iska, a zirin Gaza, wanda a sakamako hakan, mutane da dama, su ka ji raunuka.

Jim kaɗan kamin wannan rikici, shugaban hukumar palestinawa Mahamud Abbas, ya ƙi amincewa da naɗin da gwamnatin hamas ta yi wa,Djamal Abu Samhadana, mai tsatsauran ra´ayi, a matasayin shugaban rundunar yan sanda.

Shugaban Hamas, Khaled Mechaal, ya soki Abbas da kakkaussan lafazi, a dalili da wannan mataki, da ya ɗauka.

Ya dangata shi, da ɗan amshin shatan Amurika da Turai.

Wannan kalamomi, sun hadasa zanga zanga, daga magoya bayan jam´iyar Fatah ta Mahamud Abbas.

A sakamakon ganawa tsakain ɓangarorin 2, an cimma mataki ɗaya, na kwantar da hankulla da kuma haɗin kan Palestinawa domin fuskantar Isra´ila.