1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sweden ta yi watsi da zargi kan Assange.

May 19, 2017

Yan sandan Birtaniya sun ce za su kama shugaban shafin kwarmata bayanai na WikiLeaks Julian Assange bisa keta sharudan belinsa idan har ya fito daga ofishin jakadancin Equador inda yake mafaka.

https://p.dw.com/p/2dFaR
Julian Assange Gründer WikiLeaks
Hoto: picture alliance/empics/D. Lipinski

Yan sandan Birtaniya sun ce za su kama shugaban shafin kwarmata bayanai na WikiLeaks Julian Assange bisa keta sharudan belinsa idan har ya fito daga ofishin jakadancin Equador, bayan da Sweden ta yi watsi da zargin fyade da ake tuhumarsa da aikatawa.

Shi dai Julian Assange dan kasar Australia ya nemi mafakar siyasa ne a ofishin jakadancin Equador da ke London a shekarar 2012 bayan da wani alkali ya bada umarnin tasa keyarsa zuwa Sweden domin fuskantar tuhuma kan zargin fyade da cin zarafi ta hanyar lalata.

Yan sanda sun ce an bada sammacin kama Assange a shekarar 2012 bayan da ya ki mika kansa. A saboda haka yan sandan Birtaniya na da ikon aiwatar da umarnin sammacin da zarar ya bar ofishin jakadancin na Equador.

Assange dai ya dage cewa zargin da ake yi masa yana da nasaba da siyasa kuma yana fargabar cewa tasa keyarsa zuwa Sweden ka iya kaiwa ga mika shi ga hukumomin Amirka kan fallasa bayanai da shafin WikiLeaks yayi na sirrin sojin Amirka dana diplomasiyya.