Switzerland: Layin dogo mafi tsawo a duniya
June 1, 2016Talla
Shugaban kasar Switzerland Johann Schneider-Ammann ya bude sabon layin dogo na karkashin kasa a kasar da ke kira Gotthard-Tunnel. Jiragen biyu dauke da mutane 500 suka tashi daga arewa da kuma kudu na layin dogon mai nesa kilomita 57 da kuma ke zama irinsa mafi tsawo a duniya. Shugaban ya yaba da bude hanyar da wata rana ta tarihi. An dauki tsawon shekaru 17 ana aikin layin dogon da ya ratsa karkashin tsunukan Alps. Aikin ya ci kudi Euro miliyan dubu 11. Hanyar za ta rage lokacin tafiya tsakanin biranin Zürich a Switzrland da Milan a Italiya da kwatankwacin awa daya, za ta kuma saukaka sufurin jirgin kasa tsakanin kasashe da ke kusa.