1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Switzerland ta karɓi 'yan Uighurs

March 24, 2010

Wasu Sinawa 'yan ƙabilar Uighurs guda biyu, da aka a sako daga sansanin Guantanamo sun isa ƙasar Zwitzerland.

https://p.dw.com/p/MawA
Wani fursuna a GuantanamoHoto: AP

Wasu Sinawa 'yan ƙabilar Uighurs guda biyu da aka sako daga gidan yarin Amirka dake Guantanamo Bey a kasar Cuba, sun isa ƙasar Zwitzerland. Mutanen biyu waɗanda aka tsare har na tsawon shekaru takwas ba tare da kaisu kotu don tuhumarsu da aikata wani laifi ba, za su fara sabuwar rayuwa a ƙasar ta Switzerland. Wannan kasar dai ita ce ɗaya daga ƙasashen da suka amince su karɓin tsarrarun Guantanamo, a wani shirin gwamnatin Amirka mai ci, na rufe gidan yarin wanda ke cike da kace nace. ƙasar China wanda ta ɗauki mutanen biyu a matsayin 'yan ta'adda, ta soki manufar ƙasar Switzerland na karɓan mutanen, kana China ta nemi da a mayar mata da mutanen ƙasar ta., don hukuntasu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Muhammad Nasiru Auwal