1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Syria da Labanon

Ibrahim saniApril 25, 2005

Dabarwar siyasar da ake ciki a tsakanin kasar Syria da Labanon

https://p.dw.com/p/BvcK

Hausawa dai kance rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya.bayan wani dogon lokaci da aka dauka ana cece kuce game da jibge dakarun sojin kasar Syria a Labanon,rahotanni da suka iso mana a yanzu na nuni da cewa a daren jiya ne kasar ta Syria ta kammala janye dakarun nata daga kasar ta Labanon.

Idan dai za a iya tunawa a kusan farko farkon watan nan da muke ciki ne gwamnatin ta Syria ta amince da janye dakarun nata daga kasar ta Labanon sakamakon matsi data fuskanta daga kasashen ketare,usanmamma bisa kisan gillar da akayiwa tsohon faraministan kasar wato Rafik Hariri a cikin watan fabarairu n daya gabata.

Wadanda suka ganewa idon su lokacin fitar sojin daga kasar sun shaidar da cewa, sojojin sun kokkona takardun da basu da amfani da kuma rurrushe gine ginen su dake yankin Bekaa.

Bugu da kari,bayanai sun rawaito cewa a kalla motoci 15o ne aka gano na dauke da sojojin da kuma kayayyakin su.

Rahotanni dai sun rawaito cewa duk da haka ana sa ran ficewar ragowar sojojin kasar na Syria na karshe a ranat talatar nan mai zuwa idan Allah ya kaimu,.

Har ilya yau rahotannin sun nunar da cewa za a rufe iyakar kasashen biyu da zarar bataliyar sojin karshen sun yi ban kwana da kasar a ranar ta talata.

Kasar dai ta Syria ta aike da sojojin nata ne izuwa kasar ta Labanon a shekara ta 1976 jim kadan bayan kammala yakin basasa a kasar.

Gamasassun bayanai dai sun shaidar da cewa kasar ta Labanon ta fada ne cikin rigin gimu na siyasa a tun bayan kisan gillar da akayiwa tsohon faraministan kasar da wasu da suka wuce a kalla dozin daya.

A waje daya kuma awowi kadan da janye rundunar sojin ta Syria dake kasar ta Labanon kwatsam a yau litinin sai babban jamiin tsaron kasar wato Jamel Al Sayyed ya bayar da sanarwar yin murabus daga kujerar sa.

Idan dai za a iya tunawa a makon daya gabata Jamel Al Sayyéd yace zaiyi murabus daga mukamin sa idan mdd tazo gudanar da bincike na kwakwaf game da rasuwar Rafik Hariri,wanda hakan ya janyo zanga zangar bore daga alummar kasar ga gwamnatin kasar ta Syria.

A bisa ire iren wadan nan zanga zanga ne ya haifar ala dole gwamnatin kasar ta Labanon dake da goyon bayan Syria ta ruguje.

A can baya dai dama masu zanga zangar sun bukaci murabus din babban jamiin tsaron kasar a hannu daya kuma da gudanar da bincike na sanin dalilin tashin bom din da yayi sanadiyyar ajalin tsohon faraministan da kuma wasu da daman gaske.

Da yawa dai daga cikin yan kasar ta Labanon na kallon Jamel Al Sayyed ne a matsayin dan koron kasar ta Syria wanda dashi ne a ganin su kasar ta Syria tayi musu kaka gida a cikin al,amurran su na cikin gida na yau da kullum.

A daya hannun kuma bayanai sun shaidar da cewa a ranar talatar nan mai zuwa yan majalisun dokokin kasar zasu gudanar da zama don kalailaice sunayen da sabon faraministan ya mika musu don amincewa kafin kafa sabuwar gwamnatin.

Idan dai an amince da wan nan sabuwar gwamnatin daga nan ne kuma za a fara shirye shiryn gudanar da zaben gama gari a karshen watan mayu na wan nan shekara da muke ciki.