1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Syria ta amince a yiwa jami´anta tambayoyi a birnin Vienna

November 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvJP

Bayan matsin lamba da ta sha daga kasashen duniya, Syria ta amince a yiwa manyan jami´anta tambayoyi dangane da kisan gillar da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri. Wata sanarwa da gwamnati a birnin Damaskus ta bayar ta ce yanzu jami´an MDD ka iya yiwa mutane 5 tambayoyi a birnin Vienna. Syria da hukumomin MDD sun shafe makonni suna takaddama game da wurin da za´a yi tambayoyi. A cikin wani kuduri da ya zartas kwamitin sulhu na MDD ya bukaci Syria da ta ba da cikakken hadin kai ga mai shigar da kara na Jamus Detlev Mehlis. A kuma halin da ake ciki kungiyar kasashen Larabawa ta yi gargadin cewa ka da a mayar da Syria saniyar ware matukar babu wata shaida da ta tabbatar da hannun kasar a kisan da aka yiwa tsohon FM na Lebanon.