1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Syria ta watsi da kotun mussamman a kan mutuwar Hariri

June 1, 2007
https://p.dw.com/p/BuK6

Ranar laraba da ta gaba ta ne, komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia, ya kaɗa ƙuri´ar amincewa da girka wata kotu ta mussamman, da zata gudanar da bincike, da kuma yanke hukunci ga masu alhakin kissan tsofan Praminsitan Libanon Rafik Hariri.

Ƙasashe da dama, da su haɗa da Amurika, na zargin Syria da kitsa wannan kissa, zargin da hukumomin Damascus, su ka mussanta.

Bayan girka wannan kotu, Syria ta ce ba zata bada haɗin kai ba, ga ayyukan wannan kotu, wadda a tunanin Syria an girka ta ne da mumunar manufar tozarta hukumomi kasar.

Minisatn harakokin wajen Syria, Walid Mouallem, da ya bada wannan sanarwa, ya nunar da cewa, kotun ta mussamman, ba ta da wani alfano, ga yunƙurin binciko gaskiya a game da mutuwar Rafik Hariri.

Su ma ƙasashen Russie, Sin, Afrika ta Kudu , Indonesia, da Qatar, membobi a komitin sulhu, sun yi watsi da wannan kotu.