1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Syria ta yanke hulɗar diplomasiyya da Faransa

Zainab MohammedJanuary 2, 2008
https://p.dw.com/p/CjOW

Syria ta sanar da yanke dangantakar Diplomasiyya da Faransa ,wanda keda nufin kawo karshen rigingimun da Lebanon ke fama dasu.Gwamnatin Faransa dai na zargin Damaskus da haifar da tsaiko wajen cike giɓin shugaban kasar Lebanon,tare da kawo karshen janyewa daga gwamnatin da ‚yan adawa suka yi.Minisatan kula da harkokin waje na Syria Walid al-Moualem,ya fadawa manema labaru ba birnin Damascus cewar,Faransa neman ɗorawa Syria alhakin gazawar ta ,na kawo karshen rigingimun Libanon.Adangane da hakane ta dakatar da dukkan dangantakar diplomasiyya da ita.A makon daya gabata nedai shugaba Nicholas Sarkozy na Faransan ya umurci gwamnatinsa data dakatar da duk wata hulɗar diplomasiyya da Syria,adangane da abunda ya danganta da gazawan Syria wajen gano bakin zaren warware rigingimun,bayan watannin biyu na tuntuɓar juna da Faransan.