1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙadama tsakanin Libiya da Ingila

August 20, 2010

Ingila ta gargaɗi hukumomin Libiya da kada su kuskura su gudanar da shagulgulan zagayowar cikkar shekara guda da sakin Abdelbaset al-Megrahi

https://p.dw.com/p/OsWx
Abdel Baset al-MegrahiHoto: AP

Gwamnatin ƙasar Britaniya ta yi kashedi ga ƙasar Libiya wajan gudanar da bukukuwan zagayowar cikar shekara guda da sakin Abdelbaset Al-Megrahi.

Mutuman da ke da alhakin kai hari Lokerbie a shekara ta 2001 wanda a cikinsa mutane 270 suka rasa rayukansu.

Wani mai magana da yawun gwamnatin ya bayyana cewa duk wani shagali da hukumomin ƙasar ta Libiya zasu shirya zai zama tamkar zagi ga ƙasar. 

An dai saki Al-Megrahi ne a cikin watan Augusta na shekara bara daga wani gidan bursunan da ake tsare da shi a ƙasar Ekosiya, kan hujar cewa ba zai yi  watanni ukku ba a raye

Tun da farko dai friministan Britaniyan David Cameron ya shaida cewa sakin na al-Megrahi wani babban kuskure ne

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita       : Zainab Mohammed Abubakar