1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga zangar yan Adawa a ƙasar Thailand

Abdullahi Tanko BalaNovember 26, 2008

Dubban masu zanga zanga a Thailand sun mamaye babban filin jiragen sama na birnin Bangkok wanda hakan ya tsayar da alámura cik.

https://p.dw.com/p/G2RK
Ɗaruruwan masu zanga zanga a filin jirgin saman Suvarnabhumi a birnin Bangkok waɗanda ke daáwar neman Firamista Somchai Wongsawat ya yi murabus.Hoto: AP

A halin da ake ciki masu zanga zangar sun yi dafifi a filin jirgin saman Bangkok baya ga shigaye da suka sanya a manyan hanyoyi domin hana zurga zurga da kai komon ababen hawa. Wannan taƙaddama dai ta sanya an rufe filin jirgin saman ɗungurungum, yayin da dubban fasinjoji da yan awon buɗe idanu suke zaman jiran tsammani. Daraktan filin jirgin saman ya shaidawa yan jarida cewa fasinjoji kimanin 3,000 na nan sun yi carko-carko babu damar tashin jirgi. Matafiyan waɗanda suka fuskata sun koka cewa basu sami abinci ko wani abun sha ba tun da masu zanga zangar suka afka filin jirgin wanda ya tsayar da alámura cik.

Gidan Talabijin na Thailand din ya ruwaito cewa aƙalla mutane goma sha ɗaya suka sami raunuka yayin wata arangama tsakanin yan adawar da magoya bayan gwamnati. Ɗaya daga cikin shugabannin jamíyar adawar Chaiwat Sinthuwong tace ba zasu saurara ba har sai gwamnatin ta yi murabus."Tace babu gudu ba ja da baya, sai mun dakatar da haramtaccen tsarin su. Za mu yi dukkan bakin ƙoƙari wajen tilastawa gwamnati ta gyara zamanta sannan ga jamaár gari mu nusar dasu cewa lokaci yayi da ya kamata gwamnatin tayi murabus.

Artabu da kuma hare haren bama bamai a wasu sassa na birnin Bangkok na ƙara tsananta rashin bin doka da oda da kuma kakkausar adawa da Fiaraministan ƙasar Somchai Wongsawat wanda yan adawar suka ce ɗan koren tsohon Firaminista ne Thaksin Shinawat. Rahotanni sun ce aƙalla bama bamai biyu suka fashe a filin jirgin saman. Mutane uku suka jikata sai dai babu wanda ya rasa ransa. An ruwaito cewa wani bom ɗin ya fashe a tsohon filin jirgin sama na Don Muang dake zama matsuguni na wucin gadi ga gwamnatin bayan da magoya bayan jamíyar adawa ta Allaiance for Democracy suka mamaye fadar gwamnati dake babban birnin ƙasar a yan watannin da suka gabata.

Masu zanga zangar sun ce ba zasu yi zaman shawarwari da kowane jamiín gwamnati ba sai da shi kan sa Firaministan. A yau ne dai Firaminista Somchai Wongsawat ya dawo daga Peru bayan halartar taron ƙungiyar cigaban tattalin arzikin ƙasashen Asia da Pacific, ana kuma kyautata tsammanin zai kafa dokar ta ɓaci a ƙasar.

Wata daga cikin masu zanga zangar ta yi bayani tana mai cewa."Tace har yanzu bamu cimma burin mu ba, amma dai ina tsammanin mun sami yan nasarori. Wannan dai shine kusan mataki na ƙarshe, an ɗan sami rauni a gwagwarmayar da muke yi saboda bamu da isasun kuɗaɗe na tafiyar da harkokin gwagwarmayar yayin da a waje guda gwamnati ke samun maƙudan kuɗi daga kuɗaɗenmu na haraji.