1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama kan zaɓen Sudan

April 18, 2010

Jam'iyun adawa a Sudan za su yi watsi da sakamakon zaɓen ƙasar

https://p.dw.com/p/MzQ2
Tsohon shugaban Amirka Jimmy Carter, a hagu, yana ganawa da shugaban Sudan Omar al-Bashir, a damaHoto: AP

Jam'iyun adawa a Sudan sun ce ba za su amince da sakamakon zaɓukan jam'iyu da yawa na farko a ƙasar cikin shekaru gwammai ba, suna masu zargin tabƙa maguɗi. Waɗannan kalaman sun biyo bayan jawaban da masu sa ido a zaɓe na tarayyar Turai suka yi ne cewa zaɓen ya gaza cimma matsayin zaɓe na ƙasa da ƙasa, amma a lokaci ɗaya suka yi kira da a amince da sakamakonsa. Shugabar tawagar 'yan sa ido ta tarayyar Turai, Veronique de Keyser ta rawaito cewa an tabƙa kurakurai a zaɓukan na kawanaki biyar, musamman inda aka fuskanci matsalolin aikewa da kayan zaɓe da kuma janyewar da 'yan adawa suka yi. Zaɓen dai shi ne na farko a Sudan tun shekara ta 1986, wanda kuma ko shakka babu shugaba mai ci Omar al-Bashir zai yi nasarar yin tazarce.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadissou Madobi