1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama tsakanin Iran da Saudiyya

Hein,Matthias/MNA/AHJanuary 7, 2016

Tsamin dangantaka tsakanin kasashen Saudiyya da Iran da yanzu haka ke Ƙara yin muni, ya dakushe kyakkyawan fatan da aka yi na warware rikice rikicen da ake fama da su a Ƙasashen Siriya da Yemen cikin lumana.

https://p.dw.com/p/1HZmd
Iran Ibrahim al-Jaafari und Mohammad Javad Zarif
Ministocin harkokin waje na Iran da Saudiyya Ibrahim al-Jaafari da Mohammad Javad ZarifHoto: Getty Images/AFP/A. Kenare

Wannan ba shi ne karo na farko da ƙasar Saudiyya ta katse hulɗar diplomasiyya da Iran ba. A 1988 hakan ta taɓa faruwa, inda a wancan lokaci ma an kai hari kan ofishin jakadancin Saudiyya ne a birnin Teheran. Amma sun ɗinke ɓarakar da ke tsakaninsu a 1990 lokacin da Saddam Hussein da ke zama abokin gabansu ya tura sojojinsa suka mamaye Kuwaiti.

Tasirin wannan taƙaddama a yankin baki ɗaya

Bambamcin da wancan lokacin, takaddama a yanzu tsakanin Saudiyya da Iran na da babban tasiri a yankin gaba daya, domin Ƙasashen biyu sun yi dumu-dumu a yaƘin da ake yi a Siriya da Yemen da ma rikicin ƙasar Iraƙii.Julian Barnes-Dacey na majalisar hulɗa da ƙasashen ƙetare ta Turai, ya ce duk wani fatan samun ci gaba a ƙoƙarin warware rikicin Siriya ya dogara ga kyakkyawan dangantaka tsakanin Saudiyya da Iran. "Wannan gaba tsakanin ƙasashen biyu za ta mayar da hannun agogo baya ga fatan samun ci gaba a tattaunawar zaman lafiya. Ina gani a bayyane yake cewar duk fatan samun masalaha a rikicin Siriya na tsawon lokaci ya dogara kan Saudiyya da Iran su magance rikici tsakaninsu. Sai dai abubuwan da ke faruwa yanzu sun dakushe wannan fata." Ko da yake Saudiyya ta jaddada cewar ba za ta janye daga tattaunawar ba, amma Sebastian Sons na ƙungiyar nazarin manufofin ƙetare ta Jamus ya nuna shakku ga ikirarin mahukuntan na birnin Riyadh.

Saudi Arabien Jemen Krise Soldat an der Grenze
Hoto: picture alliance/abaca

Babu alamu samun haske a tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu

"Ba haske ga damarmakin da ake da su. Ko da yake ban yanke ƙauna ba cewar Saudiyya da Iran za su sake zama kan teburin sulhu. Amma ba sauran yardar tsakaninsu. Kuma duba da halin da ake ciki yanzu, zai yi wahala a samu wani sakamakon kirki a tattaunawar da Saudiyya da Iran za su shiga ciki."Kasashen biyu na gwagwarmayar karfafa ikonsu a yankin, abin da a cewar Barnes-Dacey na majalisar hulda da ƙasashen ƙetare ta Turai masu tsattsauran ra'ayi na ƙasashen biyu ke da hannu a ciki, domin suna adawa da yunƙurin samun zaman lafiya da kyautata huldar dangantaka, maikaon haka sun fi son a ci gaba da samunn rarrabuwar kai.

Saudi Arabien Trauerfeier in Al-Awamija nach der Hinrichtung von Sheikh Nimr al-Nimr
Hoto: picture alliance/AP Photo

Ci gaba da samun rarrabuwar kawuna tsakanin ƙasahen

" Hassan Rouhani na zaman wani shugaba mai son raba madafun iko a Iran. Amma yana fuskantar adawa daga masu ra'ayin riƙau da suka lashi takobin yi masa zagon ƙasa musamman a ƙoƙarinsa na fuskantar ƙasashen yamma da sauran ƙasashen yankin. Suna haɗa kai da Saudiyya domin ɓurinsu ɗaya ne wato dagula ƙoƙarin kyautata hulɗoɗin diplomasiyya."A halin da ake ciki Iran ƙasashen duniya sun buɗe kofofinsu ga gwamnatin Teheran, tun bayan da ƙasar ta yi watsi da shirinta na nukiliya. Yayin da ita kuwa Saudiyya ke fama da matsalolin tattalin arziki sakamakon faɗuwar farashin ɗanyen mai, al'ummarta kuwa na ƙara nuna takaicinsu, kana kuma dangantakarta da Amirka da sauran ƙasashen yamma ta ja baya.

Iran Protest in Teheran gegen Hinrichtung in Saudi-Arabien
Hoto: Getty Images/AFP/A. Kenare