1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama tsakanin Koriya ta Kudu da ta arewa

November 27, 2010

Dakarun Amirka da na Koriya ta Kudu na shirin gudanar da atisaye

https://p.dw.com/p/QJml
Sojojin Koriya.Hoto: AP

Sojojin ruwa na ƙasashen Amirka da na Koriya ta Kudu na shirin ƙaddamar da wani atisaye haɗin -gwiwa domin karya lagon Koriya ta Arewa. A yayin da hukumomin Koriya ta Kudu ke gudanar da jana'izar wasu dakarunsu da Koriya ta Arewan ta kashe a sakamakon hare-haren makaman atileren da ta kai akan wani tsibirin na Koriyan. Wani babban jam'in soja na Koriya ta Kudu ya shaida cewa za su ɗau fansa akan wannan rashi da suka yi na sojojinsu biyu. China ta nuna damuwa dangane da wannan atisaye ta ce ba za ta taɓa yarda ba a gudanar da shi a ƙarƙashin yanki da ta ke iko da shi.

Babban kwammandan dakarun Amirka Janar Walter Sharp wanda ya kai ziyara a tsibirin da Koriya ta Arewan ta yi lugudan wuta na makamai masu linzami ya ce da su da Majalisar Ɗinkin Duniya za su yi nazari tare kuma da yin kira ga Koriya ta Arewa da ta dakatar da kai wasu sabbin hare-hare.

Mawallafi: Abdurahamane Hassane

Edita : Halima Balaraba Abbas