1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar Iran da Amirka

August 19, 2010

Ƙasar Iran ta kawar duk wani tsammanin yin shawari, kan abinda ya shafi inganta nukiliyarta.

https://p.dw.com/p/OrY8
Ayatollah Ali KhameneiHoto: Fars

Shugaban addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khamenei yace jamhuriyar ta Islama, ba za ta shiga duk wata tattaunawa da ƙasar Amirka kan nukiliyarta ba, sai har an kawar duk wani takunkumi da barazanar soji a kanta. A wani jawabin da ya yi ta gidan talavijin ɗin ƙasar, Khamenei ya ɗorawa Amirka alhaƙin bijirewar iran ta yi, inda yanzu Iran take sarrafa kashi 20 na uraniumɗinta. A Halin da ake ciki Bankin Barclays na ƙasar Birtaniya, ya amince ya biya tarar dala miliyan 300, don saɓa takunkumin Amirka, akan ƙasashen Cuba da Iran da Sudan, a dai-dai lokacin da ƙasar Venuzuela kuwa, tace za ta ci gaba da sayarwa Iran makamashin da take buƙata, duk da barazanar da Amirka ke yiwa ƙasashe.

A wani labarin da ya danganci nuliyar Iran, shugaban ma'aikatar haɗa nukiliya na ƙasar Rasha, yace fara aikin da tashar nukilyar ƙasar Iran ta farko zai yi a ƙarshen wannan makon, ya tabbatar da cewa ƙasar Iran na iya amfani da makamashin nukilyarta, ƙarƙashin kulawar ƙasa da ƙasa. Shugaban ma'aikatar Sargei Kiriyenko ya bayyana hakanne a yau, yayinda ya ke ganawa da firimiyan ƙasar Rasha Vladimir Putin, inda yace ƙaddamar da tashar nukiliyar Iran ta Bushehr da za'a yi, zai tabbatar da cewa Rasha tana mutunta alƙawarin dake kanta. ƙasar Rasha ta karɓi kwangilar gina tashar nukiliyar tun shekaru 15 da suka gabata, amma ta yi ta jan ƙafa wajen kammalata. Iran tace dama tana buƙatar masana'antar don samarda makamashi, to amma dai ana iya amfani da masana'antar don sarrafa makaman nukiliya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu