1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar Iran da Najeriya

November 12, 2010

Iran da Najeriya na yunƙurin warware batun makaman da aka kama, a tashar jiragen ruwa na Lagos.

https://p.dw.com/p/Q6hD
Kwantenoni a tashar jiragen ruwa.Hoto: Duisburger Hafen

Gwamnatin Najeria ta ce tana samun haɗin kan ƙasar Iran a tattaunawar da suke yi kan wasu makamai da jami'an tsaron Najeriya suka kama a kwanan baya. Ministan harkokin wajen Najeriya, Odein Ojumogobia, yace a ganarwa da ya yi da takwaransa na ƙasar Iran Mounacher Muttaƙi, sun fahimci juna kuma tattaunawar ta su ta yi armashi. Tun a jiya ne dai ministan harkokin wajen ƙasar Iran Mounacher Muttaƙi ya isa Abuja don tattauna yadda za'a warware matsalar. A kwannan baya ne dai jami'an tsaron Najeriya suka kama wasu kwantenoni, ɗauke da makamai, ciki harda rokoki da gurneti da sauransu. Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya wata SSS, ajiya ta tabbatarwa manema labarai cewa, makaman dama Najeriya aka shirya kai su, ba kamar yadda ada ake raɗe raɗin cewa an nufi kai su wata ƙasa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Abdullahi Tanko Bala