1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar nukiliyar Iran.

May 16, 2010

Shugaban ƙasar Burazil yana Iran don shiga tsakani a taƙaddamar Iran da ƙasashen yamma, kan makaman nukiliya

https://p.dw.com/p/NP8P
Ahmadinejad da Lula da Silva,Hoto: AP

Shugaban ƙasar Burazil luiz Inacio Lula da Siliva yana ziyar aiki na kwana biyu a ƙasar Iran, inda ake saran batun taƙaddamar Iran da ƙasashen yamma bisa shirin Iran na nukiliya, shine zai ɗauki hankalin tattaunawar ta su. Lula zai gana da shugaban ƙasar Iran Mahmud Ahmadinajad a yau lahdi, inda ake tsammanin zai samu masalaha tsakanin Iran da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya. To sai dai ma'aikatar harkokin wajen Iran ta kawar da batun samun wata madafa, inda ma'aikatar tace za dai a taɓo batun kawai, a ɗaya daga ayyukan da shugaban Burazil ɗin zai yi. Domin shugabannin ƙasshen biyu za su inganta hulɗar tattalin arziki da haɗin kai, da kuma yarjejeniyar samar da mai tsakanin ƙasashen biyu.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal