1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddamar Wikileaks

November 29, 2010

Bayyanan sirrin da shafin internet na wikileaks ta wallafa na cigaba da haddasa taƙaddama

https://p.dw.com/p/QL1s
Shafin WikileaksHoto: picture-alliance/dpa

Shafin nan na Internet wato WikiLeaks wanda ya wallafa bayanan sirri da ke ɗauke da tattaunawa tsakanin gwamnatin Amurka da ke Washington da sauran ofisoshin jakadanci dake ƙasashen duniya na cigaba da hadassa mahawara a ƙasashen duniya. Daga farko dai bayanan sun mai da hankali ne a kan yadda jami'an diplomasiyya ke kallan halayan shugabanin duniya, inda ya yi kakkausar suka ga shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da ma Ministan kula da Harkokin Wajen Jamus Guido Westerwelle.

A halin da ake ciki yanzu, al'umma na cigaba da kushe wannan mataki na Wikileaks wanda ake ganin zai iya haddasa husumi, amma jikadan Amurka a nan Jamus Philip Murphy ya ce wannan ba zai gurbata dangantakan da ke tsakanin Amurka da Jamus ba.

Ya ce ya tabbata wannan abu ne wanda zai wuce, dangantakar Amurika da Jamus mai zurfi ce, kuma akwai ayyukan cigaba da suke yi tare, saboda haka ba za su yarda sabani ya shiga tsakanin mu ba.

Tuni dai fadar gwamnatin  White House ta yi Allah wadai da wannan lamari wanda ta kira ganganci kuma ta ce ya na tattare da hatsarin gaske.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Halima Balaraba Abbas