1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

011009 Dialog Nigeria Christen Muslime

October 6, 2009

Gangamin majami´ar Katholika a bana ana mayar da hankali kan zaman lafiya a Nijeriya

https://p.dw.com/p/K0LG

A ranar huɗu ga wannan wata na Oktoba majami´ar Katholikaa nan Jamus ta buɗe gangamin shekara shekara da za a shafe wata guda ana yi a birnin Osnabrück na nan Jamus. A wannan karo ana mayar da hankali ne akan aikin zaman lafiya da sasantawa da majami´ar ta Katholika ke yi a tarayyar Nijeriya. A kan haka majami´ar ta gayyaci limaman addinai da sarakunan gargajiya zuwa wannan taro, daga cikinsu har da Sarkin Wase mai martaba Alhaji Haruna Abdullahi da Archbishop na garin Jos Ignatius Kaigama.