1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta yaya dabbobi ke iya sajewa da wani abu

Abba BashirApril 23, 2007

Bayanin yadda Dabbobi suke boye kansu tare da sajewa da wani abu.

https://p.dw.com/p/BvUr
Miciji ya saje da launin ganye
Miciji ya saje da launin ganyeHoto: dw-tv

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun mai sauraronmu a yau da kullum, Malam Naziru Mustapha, mazauni a Birnin Kano na Tarayyar Najeriya;Malamin yana tambaya ne inda yake cewa“Bana iya hana kaina yin mamaki,a lokacin da naga irin basirar da dabbobi suke amfani da ita wajen Sajewa da wani abu lokacin da suke son boyewa wani abu da zai cutar dasu, ko kuma yayin da suke so su kama abincin su.Don haka nake so ku sanar dani, yadda Dabbobi suke samun wannan basira ta buya da sajewa.

Amsa: Daya daga cikin siffofin dabbobi wajen kare kansu, shine yadda suke boye kansu da kuma yadda suke iya canja launi su saje da wani abu.

Buya ya zama wajibi ga dabbobi saboda dalilai biyu : saboda farauta da kuma kare kansu daga farmaki.Kuma suna yin haka ne ta hanyar amfani da duk wata hanya da zata taimaka ta fuskar dabara, kwarewa, kuzari da nutsuwa.

Alal misali,kwarin bishiya suna sajewa da jikin bishiya.Haka zalika Maciji, yana boye kansa a cikin dogwayen ganye. Kwaron-mayu wanda ake kira“Caterpilla“da turanci, ya kann zauna a tsakiyar ganye don kada a gane shi.

Dabarar buya ga dabbobi tana da al’ajabin gaske. Kusan da wahala ka iya gane kwaron da ya buya jikin tumbar itace ko wata halittar dake buya karkashin ganye. Kwaron ganye na shan ruwan zakin shuka wadanda suke ciyar da kansu dashi ta hanyar zama kamar a jikin shukar suke. Ta wannan hanya ce, suke yaudararda tsuntsaye, manyan abokan gabarsu, da tabbatar da cewar tsuntsayen basu zauna a jikin bishiyoyin ba.

A cikin ruwa kuwa, akwai wani kifi da ake kiransa da suna kifi mai zarto,amma anfi saninsa da suna“Cuttlefish“ a Turance. To shi wannan kifi mai zarto, a Karkashin fatar jikin sa, akwai wata fata mai laushi tare da harza a jiki mai suna“chromatophores. Wannan fata ta shi wannan kifi tana da launuka daban-daban wadanda suka hada da launin dorawa, da ja da baki da kuma makuba . A wani lokaci, fatar sai tayi fadi kuma ta cika jikinta da inuwa.To ta haka ne kifin yake canja launi akan dutsen da ya tsaya kuma sai ya saje kamar dutsen.Haka wannan kifi yake tafiyar da wannan tsari na sajewa,idan abinda yake so ya saje dashi ja ne, to sai ya mayar da duk lanin jikinsa ja,haka idan dorawane ko baki ko kuma makuba,kasancewar a cikin ruwa akwai tsirrai daban-daban, kuma masu launuka daban-daban.Kuma duk yana yin hakanne domin ya buyar wa babban kifin da ka iya cinye shi ko kuma domin ya buyarwa abincin da yake so ya farauta.

Duk wannan dabara da hikima da wadannan dabbobi suke da su,akwai mutanen da suke ganin cewa,wai ba wani mahalicci ne ya haliccesu akan wannan tsariba, wai sun samu duk wadannan dabaru da hikimomi hakannan kwatsam ba tare da wani mahalicci da ya tsara hakan ba. Babu shakka akwai jahilci da tarin wauta ga masu irin wannan tunani. Duk wanda yayi nazarin wannan baiwa ta buya da sajewa da dabbobi suke da ita, zai tabbatar da cewa akwai wani mahalicci mai cika da kamala a cikin ikon sa, wanda ya tsara rayuwar dabbobi a irin wannan tafarki, Wato Allah subahanahu wa ta’ala,mahaliccin kowa da komai a bisa iko da nufinsa.