1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaddama game da sabbin matsugunan Yahudawa

December 24, 2007
https://p.dw.com/p/Cfgp
Sabon zagaye na tattaunawar samar da zaman lafiyar yankin Gabas Ta Tsakiya da aka shirya yi yau litinin na fuskantar ƙalubale a sakamakon taƙaddamar da ake yi dangane da faɗaɗa sabbin matsugunan Yahudawa. Shugaban Falasɗinawa Mahmud Abbas ya yi nuni da cewa ba zai yiwu Isra´ila ta ci-gaba da aiwatar da manufofinta na gina sabbin matsugunai sannan a hannu ɗaya ta yi hanƙoron samun zaman lafiya ba. Da farko dai an ministan kula da kuɗaɗen fansho na Isra´ila Rafi Eitan ya ce za a ci-gaba da aikin fadada matsugunan Yahudawa, inda ya yi nuni da cewa a cikin kasafin kuɗin shekara ta 2008, an ware kudi dala miliyan 25 domin gina sabbin gidaje 700, a Yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan da kuma Gabashin Birnin Kudus dake ƙarƙashin mamayen Isra´ila. A taron birnin Annapolis a ƙarshen watan Nuwamba, Isra´ila ta nuna shirin sake farfaɗo da shirin nan na samar da zaman lafiyar Gabas Ta Tsakiya da ake yi lakabi da taswirar hanya, wadda ta tanadi dakatar da aikin gina sabin matsugunana yahudawa a yankunan Falasɗinawa.