1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'addanci a arewacin Afurka

April 17, 2007

Hare-haren ta'addanci na yaduwa a arewacin Afurka

https://p.dw.com/p/Btvm

Kusan dukkan manazarta al’amuran yau da kullum sun dace akan cewar ta’addamnci ya fara yaduwa a arewacin Afurka. A halin yanzu an bude wani sabon babi na ta’addanci a yankin tun bayan da kungiyar ‘yan salafi mai fafutukar yada musulunci ta GSPC ta shiga fagen sauran ‘yan ta’adda na kasa da kasa. Ita kungiyar ‘yar kasar Aljeriya ce, wadda ta fara gwagwarmaya da gwamnatin kasar tun bayan kawo karshen yakinta na basasa. A cikin watan janairu da ya wuce kungiyar ta canza wa kanta suna tana mai amsa sunan kungiyar al-ka’ida ta yankin Maghreb na Musulmi. Tuni dai ta fara yada angizonta a arewacin Afurka da yankin gabas ta tsakiya, a cewar Louis Martinez, masanin siyasa a cibiyar bincike ta Faransa Ceri a takaice.

“Wani abin da za a iya lura da shi a nan shi ne kokarin bin wata manufa bai daya tsakanin dukkan kungiyoyin, wadanda suka hade kansu waje daya kama daga Tanger ya zuwa al-Kahira. Suna bakin kokarinsu wajen tabarbara al’amuran zamantakewa da tattalin arziki na kasashen yankin baki daya wadanda ke neman hada kai da KTT.”

An zabi ranar 11 ga watan afrilu ne domin koyi da 11 ga satumba da kuma 11 ga maris ta yadda ranakun 11 ga wata zasu zama abin tunawa ga jama’a. To sai dai kuma kawo yanzu ba wanda ya san tahakikanin makasudin kungiyar al-ka’idar ta Maghreb. A cikin wata sanarwar da ya bayar a cikin watan janairun da ya gabata shugaban kungiyar Abu Musab al-Wudud ya ce abokan gabarsu sun hada da Musulmi wadanda basu biyayya sau da kafa ga addini da masu adawa da musulmi, sai al’umar Faransa, wadda tayi wa yankin Maghreb mulkin mallaka da kuma na kasar Amurka, sai kuma gwamnatin kasar Aljeriya a matsayi na uku. To ko shin hakan na ma’ana ke nan masu yawon bude ido a kasashen Maroko da Tunesiya tilas su yi kuka da kansu. Wani malamin bincike daga cibiyar CERNAM, mai suna Hasni Abidi na tattare da imanin cewar akwai alka tsakanin hare-haren na Algiers da Casablanca, inda yayi bayani yana mai cewar:

“Dukkan hare-haren sun wakana ne a daidai lokacin da kasashen Aljeriya da Maroko ke fama da mawuyacin hali. Sarki Muhammed na kasar Moroko ya sallami ministoci uku na cikin gida. Mutane a Moroko na cikin matukar fargaba a game da angizon da masu zazzafan ra’ayin addini zasu samu in har an gudanar da na tsakani da Allah a kasar.”

A dai halin da ake ciki yanzun an fara samun kusantar juna tsakanin Moroko da Aljeriya don tinkarar wannan sabon yanayi na ta’addanci dake neman dabaibaye kasashen guda biyu.