1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta´addanci a birnin London

Zainab MohammedJuly 11, 2005

Halin da ake ciki a birnin London na kasar Biritaniya, game da hare haren bama baman nan da aka kai a ranar alhamis din data gabata

https://p.dw.com/p/Bvat
Hoto: AP

A yanzu haka dai a cewar kakakin gwamnatin Blair wato Tessa Jowellcewa yayi shirye shirye sun kammala na gabatar da wani sabon kudiri a gaban majalisar dokokin kasar game da batun kare aiyukan taaddanci.

A cewar kakakin idan akwai wani babban batu da za a mayar da hankali a kansa a yanzu haka a kasar shine batun amincewa da kuma aiwatar da wannan kudiri.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa ana sa ran amincewa da wannan kudiri a majalisar dokokin kasar ta Biritaniya a kusan tsakiyar shekara mai kamawa bayan anyi musayar miyau mai tsananin gaske a majalisar.

A waje daya kuma da yawa daga cikin masu nazarin siyasa ta kasa da kasa na hasshen cewa wannan kudiri ka iya samun amincewa kai tsaye a majalisar ba tare da fuskantar wata matsalaba bisa harin bama baman da aka kai a ranar alhamis din data gabata, wanda suka fasalta su da mummunan hari da turawan ingila suka taba fuskanta bayan yakin duniya na biyu.

Game kuwa da batun tuna wadanda suka rasa rayukan su a lookacin wannan hari na bama bamai, tuni gwamnatin Biritaniya ta ware wani filin shakata a kusa da kogin Thames,dake birnin na London don zama don zama dandalin nuna alhini da kuma tuna wadanda suka rasa rayukan su.

Babban dai makasudin yin hakan a cewar kakakin gwamnatin ta Biritaniya ,wato Tessa Jowell shine,na a samar da wani guri na bai daya don tunawa da mutanen da suka rasa rayukan nasu a lokacin wannan annoba.

A daya wajen kuwa magajin garin na birnin London, ya zuwa yanzu ya dukufa kain da nain wajen gudanar da kamfe na janyo hankalin mazauna birnin na London ci gaba da gudanar da rayuwar su yadda yakamata, a maimakon ci gaba da zama cikin shakku da dari dari na tsammanin murabbuka.

Game kuwa da binciken da jamin yan sanda keyi na zakulo mutanen da ake zargi nada hannu a cikin aikata wannan danyan aiki, a ya zuwa yanzu yan sandan birnin na London naci gaba da bukatar yan kasa da suka dauki hotunan yadda abin ya faru dasu aiko dasu don ko hakan ka iya taimakawa wajen gano mutanen dake da hannu a cikin na taaddanci.

Idan dai za a iya tunawa awowi kadan bayan tashin wadan nan bama bamai, yan kungiyyar nan ta Jihad dake da alaka da kungiyyar Alqeeda ta Usama Bin laden tayi ikirarin cewa tana da hannu a cikin tashihn wadan nan bama bamai.

A dai lokacin wannan mummunan hari na taaddanci, an kiyasta cewa ya jefa mazauna cikin birnin cikin rudani da dari dari banda kuma mutane sama da hamsin da suka rasa rayukan su, wasu kuma sama da dari bakwai da suka jikkata.