1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta'addanci a yankin Sahel

Tijani LawalJuly 30, 2010

A wannan makon dai kisan gillar da aka yi wa wani ɗan Faransa da ake garkuwa da shi a yankin Sahel da taron ƙolin shuagabannin ƙasashen Afirka a Uganda da kuma halin da 'yan Somaliya suke ciki a Afirka ta Kudu su ne muhi

https://p.dw.com/p/OYQw
A wannan makon shuagabannin Afirka sun gudanar da taronsu a KampalaHoto: AP

Kisan da aka yi wa Michel Germaneau ɗan ƙasar Faransa dake da shekaru 78 na haifuwa ya bayyanar a fili irin saɓanin dake akwai dangane da yaƙi da ta'addanci, kamar yadda jaridar Neues Deutschland ta nunar ta kuma ƙara da cewar:

"Bayan garkuwar da aka yi da shi har tsawon watanni uku 'yan Alƙa'idan Maghreb sun falle kan Michel Germaneau ɗan kasuwar ƙasar Faransa da aka sace a ƙasar Nijer a cikin watan Afrilun da ya wuce. Bisa ga iƙirarin ƙungiyar ta Alƙa'idan Maghreb dai tayi wannan ta'asar ce don shan fansa akan wani harin da aka kai kan 'ya'yanta kuma Faransa ce ke da alhakin wannan harin inda aka kashe 'yan ta'adda guda bakwai. Shi dai Germaneau shi ne Bature cikon na biyu da 'yan ta'addan suka kashe a watanni goma sha biyu da suka wuce."

A wannan makon ne shuagabannin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Afirka suka gudanar da taron ƙolinsu a Kampalan Uganda, inda suka tsayar da shawarar ƙara yawan sojojin kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar a Somalia. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi bitar wannan shawara da aka tsayar inda ta ce:

"A dai halin da ake ciki yanzun babu wata takamaimiyar ranar da aka tsayar a game da tura ƙarin sojojin zuwa Somaliya da kuma ƙasashen da zasu ba da gudummawar sojojin ba sai dai duka-duka abin da ƙungiyar ta bayyana fatansa shi ne samun taimakon kuɗi daga ƙasashen Turai da Amirka don gudanar da wannan aiki."

A kuma halin da ake ciki yanzu 'yan ƙasar Somaliya dake zaune a Afirka ta Kudu suna cikin hali na zaman ɗarɗar sakamakon hare-haren da ake kaiwa kan baƙi a ƙasar. Jaridar Neues Deutschland ta gabatar da rahoto tana mai cewar:

"Da yawa daga 'yan kasuwa na ƙasar Somaliya sun daina sayen sabbin hajoji saboda hali na damuwa da suke ciki a Afirka ta Kudu. A yanzu haka suna zaune ne a cikin shiri ko da rana ka ɓaci. Tun dai bayan kawo ƙarshen gasa ƙwallon ƙafa ta cin kofin duniya ne baƙi, musamman baƙar fata daga sauran sassa na nahiyar Afirka ke fuskantar barazanar hare-hare da fatattakarsu daga gidaje da kantunansu a Afirka ta Kudu".

Duk da dokar haramcin dake ci, amma fa har yau ana ci gaba da tura ruɓaɓɓun motoci daga Turai zuwa Afirka, a cewar jaridar Die Tageszeitung. Ta kuma ƙara da cewar:

"A shekarar da ta wuce an fitar da tsaffin motoci kimanin dubu sittin daga tashar jiragen ruwan Hambur zuwa ƙetare, akasarinsu zuwa Afirka. Kuma ko da yake babu wata tabbatacciyar ƙididdigar da aka bayar amma a ƙasar gaba ɗaya an fitar da motoci kimanin dubu 80 zuwa sassa daban-daban na Afirka. Kuma bana ma wannan cinikin na ci gaba da tafiya salin-alin ba ƙaƙƙautawa".

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu