Ta'addanci: Masar ta soki kasashen duniya
August 19, 2015Talla
Ma'aikatar harkokin wajen Masar din ta ce tsoma baki da kasashen suka yi katsalandan ne a harkokinta na cikin gida da kuma rashin mutunta bangaren shari'ar kasar.
Ma'aikatar ta ce ko kusa Masar ba ta sanya bakinta a kan dokokin yaki da ta'addanci da wasu kasashen su ka amince da su duk kuwa da cewar suna da matsaloli iri-iri, don haka ba ta ga hujjar tsoma baki a nata harkokin ba.
Kasashen da ke sukar wannan sabuwar doka ta Masar ciki kuwa da Amirka da wasu kungiyoyi na kare hakkin bani Adama na fargabar dokar za ta iya keta hakkin dan Adam da kuma muszgunawa kafafen watsa labarai.