1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ta´asar da Jamus ta tabka a yankin kudu maso yammacin Afirka.

Mohammad Nasiru AwalFebruary 2, 2004
https://p.dw.com/p/Bvm8
Bikin tunawa da boren na ´yan kabilar Herero da ya auku kimanin shekaru 100 da suka wuce, ya bude wani babi na tarihin Jamus, da watakila daukacin jama´a zasu fi son a barshi a rufe. Wasu kuwa na murna ne cewar za´a nunawa duniya wani babi na tarihin Jamus da ake tsoron ya fito fili. Alal misali da akwai masu zargin cewa matakan rashin imani da janar din nan na Jamus wato Lothar von Trothar ya dauka wata ta´asa ce akan wata al´uma. Shi dai janar Lothar von Trotha shi ne ya ba da umarnin murkushe boren da ´yan kabilar Herero suka tayar a yankin na Waterberg. To sai dai wani masanin ilimin tarihi da ake kira Joachim Zeller ya bayana wannan ra´ayin da cewa babban kuskure ne kuma ko kadan bai kamata a danganta abubuwan da suka wakana a ´yan shekarun nan da kuma wadanda suka faru a wancan zamani a yankin kudu maso yammacin Afirka, yankin da taba zama karkashin mulkin mallakar Jamus ba. Amma duk da haka masanin tarihin ya nuna cewa yakin kafa mulkin mallaka a Namibia daga shekarar 1904 zuwa 1908 shi ne mafarin kashe-kashen gilla da mummunan rikicin da ya auku a wannan kasa.

Ra´ayin daukacin masana tarihin dai ya zo daya cewar mulkin kama karya tare da murkushe ´yan kabilar Herero da janar din ya ba da umarnin a yi, wani nau´i ne na kisan gilla. To amma duk da haka masanan sun yi kira da a guji kwatanta wannan kisa a matsayi kisan kare dangi na mulkin mallaka, illa iyaka a kira shi yakin Herero. Masanan suka ce kamar dai a yankin na kudu maso yammacin Afirka a wasu yankunan na mulkin mallaka ma an aikata irin wannan ta´asa. Ga dokoki na shari´a ma wannan ta´asar ba ta kai matsayin kisan gilla ba, domin sai a cikin shekarar 1943 ne aka bullo da wannan kalma sannan a cikin shekarar 1948 MDD ta dauki kisan gilla a matsayin babban laifi ga ´yan Adam. Wato kenan ba´a mayar da kisan gilla a matsayin laifi ba, lokacin da Jamus ke yiwa wasu kasashe mulkin mallaka, saboda haka ba za´a iya yin kararta a gaban kotu game da wannan laifi ba. A game da haka masu shari´a a nan Jamus na ganin karar da sarkin kabilar Herero Kuaima Riruako ya shigar a gaban wata kotu a birnin Washington, inda ya ke tuhumar tarayyar Jamus da yiwa al´umar sa a wanacan zamani kisan gilla, ba zai yi nasara ba. Hakazalika ba dukkan ´yan kabilar ta Herero ke goyon bayan kira-kiraye na a biya su diyya ba, daukacinsu na bukatar gwamnatin tarayyar Jamus ta nemi gafara ne a hukumance. Wannan takaddama da ake yi game da kabilar ta Herero ta sa an manta da wata ta´asar da Jamus din ta aikata akan wasu kabilun kamar kabilar Nama, wadda sojojin Jamus suka yiwa ´ya´yanta kisan kare dangi.

Karar da ´yan kabilar ta Herero suka daukaka dai ya dauki hankalin kasashen duniya, musamman dangane da irin ta´asa da Jamus din ta yi a lokacin mulklin mallaka.