1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 10.05.2017

Mohammad Nasiru Awal
May 11, 2017

Shirin rufe kusan dukkan sansanonin 'yan gudun hijira sannan a sake tsugunar da akalla mutane dubu 10 a wasu wurare a kasar Girika.

https://p.dw.com/p/2cn66

Tuni dai aka kai wasu daga cikin 'yan gudun hijirar a wasu otel-otel a biranen kasar ta Girika suna jiran yanke hukunci game da bukatar neman mafaka da suka shigar. Birnin Thessaloniki da ke zama na biyu mafi girma a kasar ta Girika, na daga cikin biranen da aka tsugunar da bakin 'yan gudun hijira, kuma daukacin mazauna birni sun yi maraba da sabbin makwabatan na su.