1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 22.02.2017

Mohammad Nasiru Awal
February 24, 2017

Raya al'adun al'ummar Kamu da ke a jihar Gombe ta Tarayyar Najeriya.

https://p.dw.com/p/2YDPI

A ci gaba da kokarin raya al'adunta na gargajiya, a kowace shekara al'ummar Kamu da ke a jihar Gomben Najeriya tana gudanar da bukukuwa inda take tattaro 'ya'yan wannan yanki na cikin gida da na waje don gudanar da wannan biki na raya al'adu da harshen wannan al'umma da ke zama daya daga cikin kananan harsuna da ke fuskantar barazanar bacewa. Wannan kokari na bunkasa harshen al'ummar ya yi daidai da matakin Hukumar Raya Ilimi da Al'adu ta Majalisar Duniya wato UNESCO wadda ta sanya ranar 21 ga watan Fabarairu na ko wacce shekara a matsayin ranar tunawa da harshen uwa.