Taba Ka Lashe: 25.01.2017
January 27, 2017Talla
Kasar Faransa ke kan gaba a jerin kasashen yammacin duniya da a yawan 'yan kasa da suka shiga yakin Jihadi a ketare, to amma tana tafiyar hawainiya wajen kirkiro da wani shiri mai nagarta na yaki da tsattsauran ra'ayin addini. Sai dai hakan ya fara canjawa, inda yanzu haka a birnin Bordeaux na kasar ta Faransa aka fara wani hadin guiwa tsakanin mahukuntan birnin da al'ummar Musulmi don kawo sauyi.