1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taba Ka Lashe: 29.11.2017

Abdullahi Tanko Bala MNA
December 5, 2017

Tatsuniya ko labari na kunne ya girmi kaka hanya ce da magabata a cikin al'umma ke yada al'ada da cusa tarbiyya a zukatan yara da a kan ce manya gobe. Shin yaya wannan al'ada ta ke yanzu a kasar hausa?

https://p.dw.com/p/2onWv

Tatsuniya na daga cikin al'adar Bahaushe na kaka da kakanni wanda ya kunshi ba da labari na al'adun gargajiya da habaici da karin magana da raha. A takaice dai ya kunshi zamantakewa ta rayuwar al'umma. Tatsuniya ba koyar da ita ake yi a makaranta a matsayin darasi ba, sai dai iyaye da kakanni na labarta shi ga 'ya'ya ko jikoki a matsayin wani ilmi na fatar baka.