1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TABARGAZAR CIN HANCI DA RASHAWA TANA YADUWA A FANNIN WASANNIN MOTSA JIKI A JAMUS

YAHAYA AHMEDMarch 10, 2004

Batun yaduwar cin hanci da rashawa a harkokin wasannin motsa jiki a nan Jamus, na barazanar janyo gagarumin cikas ga yunkurin da kasar ke yi na samun izinin shirya wasannin Olympics na shekara ta 2012. Kazalika kuma, wannan batun ya shafi wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya da za a yi a cikin shekara ta 2006 a nan Jamus.

https://p.dw.com/p/BvlO
Karl-Heinz Wildmoser, shugaban kungiyar kwallon kafar TSV 1860 München, wanda ake zargi da karbar cin hanci, dangane da tabargazar da ta shafi ba da kwangilar gina sabon filin wasan birnin Münich.
Karl-Heinz Wildmoser, shugaban kungiyar kwallon kafar TSV 1860 München, wanda ake zargi da karbar cin hanci, dangane da tabargazar da ta shafi ba da kwangilar gina sabon filin wasan birnin Münich.Hoto: AP

A cikin shekara ta 2006 ne za a yi wasar cin kofin duniya ta kwallon kafa a nan Jamus. Amma kafin wannan lokacin ma, an fara samun tabargaza da ta shafi manyan jami’an kula da harkokin wasannin motsa jiki. Da farko dai, an zargi jami’an Hukumar birnin Leipzig ne da karbar cin hanci da rashawa, a lokacin mika takardun neman shirya wasannin Olympics da birnin ke yi. A halin yanzu kuma, wata tabargazar da ta kunno kai ta shafi zargin da ake yi wa shugaban kungiyar kwallon kafar nan ta TSV 1860 Münich, Karl-Heinz Wildmoser ne da dansa, na karbar cin hanci wajen ba da kwangilar gina sabon filin wasar Münich.

Ofishin daukaka karar jama’a na birnin na Münich, na tuhumarsu ne da nuna fiffiko da kuma bai wa wani kamfanin gine-ginen Austriya kwangilar gina filin wasar, wanda za a kashe kimanin Euro miliyan dari 2 da 80 a kansa, bayan sun karbi cin hancin kusan Euro miliyan 3. Idan dai aka tabbatad da wannan zargin a gaban kotu, to hakan zai sanya jami’an harkar wasannin motsa jiki na nan Jamus cikin wani mummunan hali. Da farko dai wannan tabargazar za ta shafa wa sunan kungiyar kwallon kafar ta TSV 1860 Münich, kashin kaza. Sa’annan kuma, za ta dusashe farin jinin kungiyar kwallon kafar FC Bayern Münich, wadda take cikin masu ba da kwangilar gina filin wasar.

Kamar yadda aka shirya dai, a wannan filin ne za a yi bikin bude wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya a shekara ta 2006. To sai ga shi kuma wannan tabargazar ta bullo, a daidai lokacin da ake neman gabatar da wata kyakyawwar hukar Jamus ga duniya, bayan karantsayin da aka samu game da rikicin keta ka’idojin kare darajar kudin Euro, wanda ya barke tsakanin Jamus da kungiyar Hadin Kan Turai.

Tabargazar ta Münich dai, na haskaka wasu bangarori ne na harkokin wasannin motsa jiki na nan Jamus, wadanda har ila yau suke cikin duhu. A galibi dai, ba kwararrun jami’ai ne ke gudanad da harkokin kungiyoyin wasannin ba. Sabili da haka ne kuma, ba sa iya tanadin dimbin yawan kudaden amanar da ke shigowa hannunsu kamar yadda ya kamata. Ta hakan ne dai alal misali, kungiyar wasar kwallon kafar nan ta Borussia Dortmund ta sami kanta cikin irin wannan tabargazar, wadda ta karya mata jari. Ba za a iya mantawa kuma da tabargazar da ta shafi kungiyar FC Kaiserslautern ba a kwanakin baya. Duk kungiyoyin biyu dai na nan na ta fama da sakamakon da irin wadannan munanan halayen jami’ansu, suka janyo musu.

A takaice dai za a iya cewa, a nan Jamus ma, fannin wasannin motsa jiki bai tsira daga illolin cin hanci da rashawa ba. A kasar da ake ta samun jam’iyyun siyasa cikin tabargazar hada-hadar kudade, da keta ka’idojin bayyana kasafin kudinsu ga majalisa, inda kuma a fannin tattalin arziki, ake ta kara samun yaduwar cin hanci da rashawa, ai ba abin mamaki ba ne, idan a harkokin wasannin motsa jiki ma, wannan illar ta kunno kai.