1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tabargazar safarar fursinoni a asurce

December 5, 2005

Rahotanni sun ce CIA kan yi amfani da harabar Jamus wajen kai fursinoni wuraren azabtar da su a ketare

https://p.dw.com/p/Bu3e
Condoleeza Rice
Condoleeza RiceHoto: AP

Tun da farkon fari ne dai Stephen Hadley, mashawarcin gwamnatin Bush akan al’amuran tsaro yayi alkawarin bin diddigin wadannan rahotannin domin tsage gaskiyar zargin da ake wa hukumar leken asirin Amurkan ta CIA na amfani da sansanonin askarawan sama na Amurka dake nan Jamus wajen safarar fursinonin da ake tuhumarsu da kasancewa ‚yan ta’adda domin azbtar da su a kasashen gabacin Turai da Afghanistan. Amma fa ba a sa ran samun wani bayani dalla-dalla daga sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice a game da wannan batu a ganawar da zata yi da kawayen Amurkan na nahiyar Turai. Shi kansa mashawarcin shugaba Bush akan al’amuran tsaro Stephen Hadley sai da ya fadi hakan a cikin wata hira da aka yi da shi ta tashar telebinjin din CNN, inda yake cewar

„Idan har gaskiya ta tabbata a game da wannan mataki na CIA, to kuwa ba zamu iya fito da maganar a bainar jama’a ba. Amurka na hadin kai da wasu kasashe a matakanta na murkushe ta’addanci da take fafutukar yi. Kuma wannan manufa ta kunshi wasu ka’idoji guda uku da suka hada da biyayya ga daftarin tsarin mulkinta da dokokinta da kuma alhakin dake kanta dangane da yarjeniyoyin dake tsakaninta da kasashen da lamarin ya shafa. Kazalika girmama ikon cin gashin kann wadannan kasashe, sannan na uku ba za a rika zirga-zirga da fursinoni zuwa wasu sassa na duniya domin azabtar dasu ba.

Babu dai wani karin bayani da Hadley yayi a game da zargin da ake yi na safarar fursinoni a asurce da CIA ke yi zuwa ketare. Mashawarcin tsaron na Amurka bai ce uffan game da haka. Bai musunta wannan zargi ba, bai kuma fito fili ya tabbatar da gaskiyar lamarin ba. To sai dai kuma ala-tilas ya hakikance da gaskiyar cewa akan yi jigilar wasu fursinonin da ake tuhumarsu da zama ‚yan ta’adda daga kasa zuwa kasa, wanda Hadley ya ce wai wani bangare ne na matakan yaki da ta’addanci. Wannan bayani kuwa na mai yin nuni ne da kokarin da mashawarcin na shugaba Bush ke yi na kwatanta wannan mataki na hukular leken asiri ta CIA tamkar lamari ne dake kann tsarin doka kuma gwamnatocin wasu kasashen na da cikakkiyar masaniya game da haka. Wannan ya sanya jaridar Washington Post a cikin wani rahoton da ta bayar a jiya lahadi ta fito fili ta bayyana cewar tsofuwar gwamnatin Jamus na da cikakken labarin wani kuskuren da aka yi na cafke wani Bajamushe a asurce a cikin watan mayun shekarar da ta wuce. Jakadan Amurka Coats ne ya labarta wa tsofon ministan cikin gida Otto Shily a game da kame wani Bajamushe haifaffen kasar Libanon da CIA tayi a Macedonia a wajejen karshen shekara ta 2003, inda aka tura shi zuwa Afghanistan domin azabtar da shi ba gaira ba dalili. Saboda daga bisani an gano cewar kuskure ne aka yi, wannan talikin baya da wata nasaba da ayyukan ta’adda.