1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tabbatar da dokar hana daura kallabi a Turkiya

November 10, 2005

Kotun kare hakkin yan Adam ta kasashen Turai, ta amince da dokar hana daura kallabi a makarantun Turkiya

https://p.dw.com/p/BvUT
Pirayim ministan Turkiya, Recep Tayyib Erdogan
Pirayim ministan Turkiya, Recep Tayyib ErdoganHoto: AP

Kotun kare hakkin yan Adam na kasashen Turai, yau ya gabatar da hukuncin sa, game da matakin da gwamnatin Turkiya ta dauka, na haramtawa mata daura dankwali, ko kallabi a jami’oin kasar. Shin ko idan aka kori dalibai daga jami’oi, saboda sun daura kallabi a lokacin karatu, hakan ya sabawa yancin addini da yancin samun ilimi. Wannan dai shine abin da wata ba-turka yar shekaru talatin da biyu ta daukaka kara kansa, a gaban kotun kare hakkin yan Adam na kasashen Turai. Yau kotun ya yanke hukuncin sa a game da karar da ta daukaka.

To ita dai ta dai wannan Ba-turka ta daukaka karar ne saboda a Turkiya, an hana ta ci gaba da karatun neman zama likita a jami’a saboda tana zuwa aji da daurin kallabi. Bayan nazari, kotun dake Strassbourg ya tabbatar da matakin haramta daura kallabi a manyan makarantun kasar ta Turkiya. Alkalai goma sha shidda ne suka goyi bayan wnanan hukunci, sa’anan alkali daya ya goyi bayan kararar da Lelya Sahin ta daukaka a gaban kotun.

Alkalan suka ce wannan mataki na hana ta daura kallabi a jami’ar birnin Istanbul, bai tauye yancin tafiyar da addinin ta ba, kazalika, bai kuma tauye yancin ta na samun ilimi a kasar ba. Fannin nan dake rubuce a tsarin mulkin Turkiya, wanda ya tabbatar da raba tsakanin al’amuran addini da na kasa, ya bada damar haramta duk wasu tufafi da suka shafi addini a makarantu ko wurare na gwamnnati a kasar. Wannan bangare na tsarin mulkin kuwa, bai keta haddin manufofin kare hakkin yan Adam na kasashen Turai ba, wadanda manufofi ne da kotun take da alhakin tabbatar da ganin an yi aiki dasu. Kotun ya kara da cewar wannan mataki na Turkiya bama addinin musulunci kawai ya shafa ba.

Lelya Sahin, wadda a shekara ta 1998 ne shugaban jami’ar ta Istanbul ya dakatar da ita daga karatun neman zama likita, saboda taki dakatar da daura kallabi a azuzuwa, ta gabatar da kara a kotuna dabam dabam. Tun shekara ta 1999 take zaune a Vienna, inda a can din taci gaba da karatun ta. A watan Yuni na bara, alkalai da suka yi nazarin farko na karar a kotun kare hakkin yan Adam, suka yi watsi da ita.

Tun a wannan lokaci, hukuncin ya haddasa muhawara mai tsanani a kasar Turkiya. Magoya bayan matakin raba al’amuran addini da na kasa, suka ce an tabbatar da wannan ra’ayi nasu, inda suke ganin kallabi ya zama wata alama ce ta tsattsauran ra’ayin na addinin Islama. Pirayin minista REcep Tayyib Erdogan a daya hannun, yana ganin cewar daura kallabi a wurare ko gine-gine mallakar gwamnati, mataki ne na tabbatar da hakkin yan Adam. Jam’iyar sa ta AK, mai ra’ayin addinin musulunci, tayi alkawari, lokacin kampe na neman zabe shekaru ukku da suka wuce, cewar zata warware matsalar ta daura kallabi.

Magoya bayan Erdogan sun nuna cewar akalla daga lokacin da aka dauki Turkiya a kungiyar hadin kann Turai, tilas ne dokar hana daura kallabin ayi watsi da ita. Suka ce a kasashen kungiyar hadin kann Turai da dama, an kyale yan makaranta da dalibai su rika daura kallabi a azuzuwan su. Hatta a kasa mai tsananta matakin raba addini da al’amuran kasa kamar Faransa, dalibai suna iya daura kallabi a jami’oi masu zaman kansu.

Kungiyar shugabannin jami’oi a Turkiya ta dade tana adawa da duk wani mataki na kokarin sassauta dokar da aka bullo da ita tun a shekaru na casa’in game da haramta daura kallabi a makarantu Shugaban kasa, Ahmet Necdet Sezer, shima dai yana lura sosai, domin tabbatar da ganin an raba addini da al’amuran kasa. Wannan ma shi ya sanya baya gaiyatar uwargidan Piraim minista Erdogan a duk lokacin da ya shirya wata liyafa, saboda Emine Erdogan, a duk inda take, bata rabuwa da kallabi a kanta.

Musamman dai wanan hukunci da kotun na kasashen Turai ya zartas yau, ranar goma ga watan Nuwamba, ya zama mai daukar hankali, saboda ganin cewar an gabatar dashi ne a kewayowar ranar da gwarzon da ya kafa Turkiya ta wnanan zamani, wato Atatürk ya rasu, wanda kuma shine tushen matakin raba addini da al’amuran kasa a cikin ta.