1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tafintar kwamfuta na Qwerty

Abba BashirDecember 19, 2006

Me yasa aka shirya Tafintar kwamfuta na Qwerty a Hargitse

https://p.dw.com/p/BvV5
Tafintar Kwamfuta
Tafintar KwamfutaHoto: AP

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawar mu ta wannan makon ta fito ne daga hannun Malam Saminu Muntari, Sokoto, Najeriya. Malamin cewa ya yi; Menene dalilin da ya sa aka shirya haruffan da suke akan Tafintar- Kwamfuta, wato Keyboard, a Hargitse?

Amsa: Tafintar kwamfiyuta na QWERTY Keyboard, shine tsararren tafintar kwamfuta na gamagari na inji mai kwakwalwa ko kuma na Tafureta wanda ake amfani da shi a harshen Turanci. Kuma ya samu wannan suna nasa na QWERTY daga haruffa guda shida wadanda suke daga farkon layin haruffa daga sama.

Shi dai tsarin Tafintar kwamfuta na Qwerty, an kirkiro shi ne a shekarar 1860, kuma sunan mutumin da ya kirkiro shi Mr. Christopher Sholes, wanda ya ke Edita ne shi na Jarida, shine kuma Mutumin da ya kirkiro da Tafureta, wato keken Rubutu.

Tun asali dai yadda aka tsara haruffan kwamfuta, an shirya su ne akan tsarin yadda haruffa suke a jere, wato daga A – Z; kuma an fara tsara sune a Tafureta, inda aka tsara kowanne harafi a jikin wani dogon karfe wanda ya ke taba takarda yayin da aka danna maballin harafin da ake bukata. To daga baya sai aka ringa samun matsaloli, kasancewar idan mutum ya kware sosai wajen saurin bugun Tafureta, sai wadannan haruffa na kusa da juna su rinka makalewa, har sai mutum ya sa hannunsa ya rabasu, kuma garin rabawar sai saitin takardar ya goce ko kuma takardar ta muttsuke da dai sauran matsaloli makamanta wadannan.To daga nan ne fa, Mr. Sholes ya ga cewar babu wata mafita ta wadannan matsaloli, illa a zauna ayi nazarin kalmomin Turanci aga haruffan da suka fi kusanci da juna domin a nesanta su da juna dai dai gwargwado. Wannan shine dalinin da ya haifar da Tafintar kwamfuta na QWERTY.

Akwai yan canje-canje da aka yi a tsarin yadda aka shirya tafintar kwamfuta a wasu harasan daban. Misali a tafintar kwamfuta na Jamusanci an kara haruffan da Bajamushe ya ke cewa Umlawut, wato harafin “Ü’’ mai digo biyu a sama da kuma harafin “Ö’’ mai digo biyu a sama, kuma an kara sune a bangaren dama na harafin “P’’ da kuma “L’’. Sannan kuma an yi canjin wuri tsakanin harafin “Z’’ da harafin “Y’’, saboda a Jamusance anfi amfani da harafin “Z’’ akan harafin “Y’’, kuma dama saboda harafin T da Z a wasu lokuta sukan zo tare a cikin kalmomin Jamusanci, sai Bajamushe ya ke kiran nasa Tafintar Kwamfutar da suna QWERTZ.

To haka dai wannan lamari yake a dukkanin sauran manya-manyan harsunan Duniya, wadanda suke da tafintar kwamfuta na haruffansu, kamar dai harshen Larabci da Faransanci da Chainisanci da Rashanci da dai sauransu.