1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tafiyar hawainiya wajen aiwatar da shirin tsuke bakin aljihu

Mohammad Nasiru AwalOctober 1, 2015

Asusun IMF ya nuna rashin gasuwa da shirin sauye-sauyen tattalin arziki a Girka, wanda ya ce gwamnati ta gaza aiwatar da shirin yadda ya kamata.

https://p.dw.com/p/1Ggg3
Griechenland Alexis Tsipras im Parlament
Firaministan Girka Alexis Tsipras lokacin wata mahawara a majalisar dokokiHoto: Getty Images/AFP/L. Gouliamaki

Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya ce ana tafiyar hawainiya wajen aiwatar da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati a kasar Girka. Mujallar "Der Spiegel" ta Jamus ta rawaito wani nazarin cikin gida na asusun IMF na cewa ko da yake tun a tsakiyar watan Yuli mahukuntan birnin Athens sun kafa dokokin da za su share wa kasar Girka fagen samun karin tallafi, amma har yanzu 'yan kalilan ne daga cikin dokokin aka aiwatar da su. Asusun ya kara da cewa har yanzu ana jiran Girka ta aiwatar da kashi biyu bisa uku na matakan yi wa tattalin arzikinta kwaskwarima. Sai dai sabon zaben 'yan majalisar dokoki a ranar 20 ga watan Satumba na zama dalilin wannan jinkiri da aka samu, wanda kuma a cewar asusun na IMF ya gurgunta tsarin lokacin ba da rukuni na uku na tallafin.