1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tagwayen harin kunar bakin wake a masallatai a Iraki

Zainab A MohammadNovember 18, 2005
https://p.dw.com/p/Bu7o

IRAK

Yan kunar bakin wake biyu sun sanadiyyar rayukan mutane 41 ,tare da raunana wasu 75,ayayinda suka tayar da bonb dake daure a jikinsu a masallatan yan darikar shia guda 2 a garin Khanaqin dake gabashin iraki,alokacin sallar jumma yau.

Rahotanni yansanda na nuni dacewa ,yan kunar bakin waken biyu sun kai hari wadannan masallatan ne adai dai lokacin da suke cike makil,ana sallar jummaa,harin daya lalata ginin masallatan.

Bugu da kari an kuma kai hari na uku a kusa da wani banki nake wannan gari.

To sai dai ana ganin cewa kasancewar garin na Khanaqin dake kann iyakai Iraki da Iran ta gabashi ,kuma ke dauke da yan shia da kuma kurdawa,zai iya haddasa barkewan sabon rikici ,gabannin zaben 15 ga watan Disamba,zaben da Amurka ke ganin zai haifar da zaman lafiya tare da ingantacciyar democdaiyya shekaru biyu da rabi ,bayan mamayan datayi wa jagoranci.

Bugu da kari da safiyar yau ne wani yunkurin kai hari wani babban hotel a birnin bagadaza,harin da a maimakon haka ya ritsa da ginin wani gida,inda nan ma mutane 6 suka rasa rayukansu.